Sarkin Kano Yayi kira Da Yin Aiki Da Gaskiya Da Adalci Don Inganta Rayuwar Duniya Da Lahira.

Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)

Jiya Alhamis 25/11/2022, Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya karbi bakuncin Shugabannin cibiyar Koyan Zayyanar Zadarwa IGC wato (Institute Of Graphic Communication) dake a jihar Kano da kuma kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Da Walwalarsa, suma da suke a jihar Kano.

Shugabannin sun ce sun kowa ziyarar bangirma fadar Maimartabar ne don neman sanya albarkar Sarkin da kuma neman goyon baya akan ayyukan su. Yayin da suka bayyanawa Sarkin ire-iren aikace-aikacan da suke gudanarwa.
Da yake maida jawabi, Maimartaba Sarkin ya yabawa hukumomin bisa yadda suke aiyukan su da kuma kira garesu da suci gaba da aiyukan su cikin gaskiya da adalci, don samun rayuwa ingantaccen a duniya da lahira. Kuma ya bayyana goyon bayan masarautarsa inda yace kofarsa a bude take a koda yaushe, wajen bayar da gudumawa da shawarwari wajen samar da cigaban al’umma a jihar Kano da kasa baki daya.

Daga karshe ya yaba musu bisa ziyarar da suka kawo fadarsa sannan yayi musu fatan alheri a cikin aiyukana su.

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post