Daga Abdulnasir Yusuf Ladan
"Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dawo cigaba da rajistar masu kada kuri’an ba tare da wani bata lokaci ba, har zuwa kwanaki 90 kafin babban zaben shekarar 2023.
"A hukuncin da ya yanke mai shari’a Inyang Ekwo, ya kuma umurci hukumar ta INEC da ta tabbatar da cewa ba a hana ‘yan Najeriya da suka cancanta ba damar samun katin zabe a zabe mai zuwa.
"Mai shari’a Ekwo ya ce alhakin da tsarin mulki ya dora a wuyan hukumar zabe shi ne ta samar da isassun kayan gudanar da zaben kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada.
"Kamfanin dillancin labaru na Najeria NAN ya ruwaito cewa Anajat Salmat da wasu mutane uku sune suka kai karar INEC akan batun.
"Afarkon korafin da suka gabatar a gaban kotun, masu shigar da kara sun ce lokaci bai yi ba da INEC zata dakatar da cigaba da rajistar katin zabe sabanin yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
"Sun bukaci kotun da ta umarci hukumar zaben da ta gaba da gudanar da aikin rajistar kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Inuwar Labarai RPT 001
