Daga Abdulnasir Yusuf Ladan
An gurfanar da wani mutum a jihar Adamawa da laifin sanya tufafin mata don yaudarar maza dan amsar kudin su.
Mutumin mai suna Muhammed Abubakar ya ce ya saba sa kayan mata kuma yana fita da abokansa mata domin samun kudi a wajen maza masu bukatar soyayya.
Muhammed wanda ke da shaidar difloma a fannin kasuwanci daga kwalejin kimiyya da fasaha ta adamawa, yola, ya ce matan da suke yi masa aiki sun ba shi tsakanin N500 zuwa N1,500 a kullum a matsayin kason sa.
Muhammed, wanda ya ce yana amsa sunan mace na fadi, ya shaida wa babbar kotun majistare da ke Girei inda aka gurfanar da shi a gaban kuliya, cewa abokansa mata sun kasance suna kare shi a duk lokacin da wani namiji ya so ya dandana shi, ta hanyar gaya wa mutumin cewa ita (shi). tana cikin hailarta.
Wakilin jaridar The Nation, ya samu labarin cewa basajar muhammed ya kare ne a ranar 16 ga watan Nuwamba a kasuwar Girei inda ya je sayan zoben kunne sai wani mutum ya gan shi wanda ya yi zargin cewa shi namiji ne.
Mutumin da yake tuhuma ya ankarar da mutane aka kama shi.
Kotun da ke karkashin jagorancin martina gregory ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 5 ga watan Disamba.
Inuwar Labarai RPT 001
