Kungiyar Tsangayu Ta Kasa Reshen Jihar Jigawa Ta Bukaci Malamai Da Almajirai Su Mallaki Katin Zabe.

Daga Abubakar M Taheer.

Kungiyar Malaman Tsangayu Ta Jihar Jigawa ta bukaci Malamai da Almajirai su Mallaki Katin Zabe domin zabar shuwagabanni na gari.
Shugaban Kungiyar na Jiha Malam Ibrahim Mai Bingida ne yayi wannan Kira a Taron da suka gabatar na wakilansu dake fadin kananan hukumomi 27 na Jihar Jigawa.

Malam Ibrahim Ya Kara da cewa a yanzu sama da Malamai da dalibai sama da Mutum dubu Dari biyu suka yi rijistar Zabe.


Malam Ibrahim ya Kara da cewa Wannan ne zai Basu dama ga gana da 'Yan takara domin sanin alkawuran da zasu musu domin ciyar da lamarin Tsangaya gaba.
Dayake Jawabi Sakataren Kungiyar Goni Suhailu Gumel yace sama da shekara 18 da kafuwar Kungiyar Wanda lamarin Kama Almajirai a 2019 ne ya Kara farkar dasu suka sake zage damtse domin cigaba da fito da martaba makaranta Al'qurani.

Goni Suhailu ya Kara da Kira da sauran membobin Kungiyar dasu cigaba bada hadin kai domin cigaban tafiyar.

Anasa jawabin Malami daga Jami'ar Sule Lamido Dr.Abubakar Maje Ya Bukaci a Samar da hukumar da zata kula da Almajirai da yaran da basa zuwa makaranta.

Dr.Abubakar Ya bayyana cewa zasu rubuta takarda su aikewa jami'ar Sule Lamido Kafin Hausa domin Samar da cibiyar nazarin karatun Al'qurani Kamar ta Jami'ar Bayero.

A karshe aka gudanar da karatun Al'qurani Mai girma tare da daukan hotuna da mahalarta Taron.

Post a Comment

Previous Post Next Post