Wara zarkadediyar matashiya, haifaffar Najeriya ta kashe kanta saboda mahaifiyarta ta ki amincewa tare da karbar saurayin da take so.
Yarinyar, Taiwo mai shekara 17 a duniya, ta kashe kanta ne saboda mahifiyar ta hana ta ci gaba da ganin saurayinta, dan shekara 19 da ya kammala makarantar sakandare a shekarar 2021.
An ce Taiwo ta saka wani abu mai guba a cikin abin sha da take sha a ranar Juma’a, 21 ga Oktoba, 2022. Mutuwarta ta faru ne a unguwar Dalemo Alakuko da ke Legas a ranar da ta sha gubar.
A cewar wasu bayanai, dalilin da yasa Taiwo ta kashe kan nata ba shi da alaka da rayuwar soyayyar ta.
Saidai jami'an tsaro sun dukufa tare da kame mahaifiyar yarinyar don gano musabbabin lamarin.
Tags:
Soyayya
