Amnesty ta soki hukuncin da aka yi wa su Mubarak Uniquepikin

Aliyu Samba

Kungiyar dake rashin kare hakkin bil'adama ta yi suka akan hukuncin da wata kotu tayi wa matashin nan mai barkwanci a TikTok wanda aka fi sani da Mubarak Uniquepikin. 

A makon nan ne kotu tayi hukuncin bulala 20 da kuma sharar harabar kotu na tsawon wata guda, Æ™ari akan tarar kudi Naira 20,000 bisa laifin yin wani barkwanci da akai karar su akai cewa sun yi kalmomin batanci ga Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. 

Sakon na Amnesty International da ta wallafa a shafin Tuwita yana dauke da wani bidiyo da kira kan lallai a soke wannan hukuncin da akai wa matasan. 

"Dole ne a soke wannan zaluncin da akai wa yan TikTok, kuma dole ne a sake su nan da nan ba tare da wani sharadi ba" inji Amnesty International. 

Mubarak ya fuskanci tuhuma ne bayan yaɗuwar wani gajeren bidiyo nashi da maja baƙin sa, inda sukai amfani da wani salo kamar na masu wa'azi wajen gabatar da kalmomin da aka gabatar da su gaban kotu a Matsayin cin mutunci ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

🎥 Twitter/Amnesty International

Post a Comment

Previous Post Next Post