SIYASA: Ku guji furta kalamai marasa Dadi akan rikicin Garo da Doduga a Kano--Hon. Ungogo

Daga Ibrahim Hamisu

Shugaban kungiyoyin magoya bayan mataimakin Gwmna kuma dan dan takarar Gwamnan Kano a APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna Hon Alh Aminu Saleh Ungogo ya yi kira da jan hankali ga dukkanin masoya bayan Dr. Nasir Yusuf Gawuna da Hon Murtala Sule Garo da masoya Hon Alhassan Ado Doguwa da Jam'iyyar APC mai Albarka da su guji furta ko yada kalamai marasa dadi ga kowanne bangare sakamakon Sabanin daya faru

Kazalika Hon Ungogo ya kara Barranta Gamayyar kungiyoyin Gawuna Coalitions Forum ga Dukkanin wata fitina a siyasance kana ya ce kowanne Bangare daya maida hankali wajen hada kan Jam'iyyar APC a Lungu da sako na jihar kano,

Sannan yakara jan Hankali a kan aguji duk wani nau'i na maganganu marasa ma'ana,

Ta cikin wata sanarwa da jami'in hurda da jamaa na hadakar Abubakar Salihu Badamasi ya fitar ta ce Hon. Ungogo yayi kira da kira ga 'yan Media na Radio da kafafan sada Zumunta da suji tsoron Allah su guji yada Fitina a maganganunsu a baki da Rubutunsu.

Sannan ya yi addu'ar samun nasara ga Jam'iyyar APC a zaben 2023 a Kano da ma kasa baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post