Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)
Rundunar Ƴan Sintiri ta Vigilantee ta jihar Kano ta kamo wani matashi mai suna Mukhtar Isa mazaunin unguwar Jakara bisa zargin sa da satar man gyada jarka 6 da manja jarka 3, wanda a jimullar jarka 9.
A zantawar mu da Mukhtar shin ko a ina ya sato wannan mai? Nan take ya bayyana inda ya sato da kuma abokin aika-aikar nasa, amma sai dai abokin nasa ya cika wandonsa da iska sai.
Wakilin namu ya zanta da babban Kwamandan ƴan sintiri na jihar Kano Alhaji Shehu Rabiu ko yaya za suyi da wannan mai da kuma matashin da suka
yi Ram da shi a komar tasu?
Sai yace "zamu kammala bincike sannan mu kai shi Hukumar ƴan sanda su kuma su gurfanar dashi a kotu"
Shehu Rabiu yace da zarar sun kammala bincike zasu mika shi ga jami'an ƴan sanda na ofishin anti daba domin fadada bincike.
A karshe yayi kira ga jama'a dasu dinga kula da shagunan su a duk lokacin da suka tashi zasu rufe domin gudun shigar barayi.
