SIYASA: Ƴan PDP sun wanke filin da APC ta ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jos


Daga Abdulnasir Yusuf Ladan

A yau Laraba ne dai da yawa daga cikin mazauna garin Jos, musamman matasa  magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP su ka yi farin-ɗango zuwa filin wasa na Rwang Pam, inda aka kaddamar da yakin neman zaben shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, domin wanke filin.

Matakin nasu ya zo ne sa’o’i 24 bayan da jam’iyyar ta APC ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a babban birnin na jihar Plateau .

Da dama daga cikin kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar PDP da ke cikin matasan, sun ce matakin da suka dauka shi ne don nuna aniyarsu ta korar APC a Plateau a zaɓe mai zuwa.

Kamru Sani, Darakta Janar na kungiyar Atiku Motivational Movement, wanda ya bayyana haka, ya ce an dauki matakin ne domin a share rashin nasarar da APC ta kawo jihar.

Sani ya bayyana cewa Plateau tungar PDP ce, kuma tana shirin komawa kan hanyarta ta samun nasara.

"Mun zo nan ne domin mu kawar da duk abin da suka kawo nan, kamar yadda PDP ta kasance ta Filato da Najeriya."

“Jam’iyyar na shirin sake samun nasara, domin ta nuna cewa ita ce jam’iyya ta gaskiya a jihar.

"Jam'iyyar za ta kawo sauki ga wahalhalun da 'yan jihar da Najeriya suka sha a cikin shekaru bakwai da suka wuce," in ji shi.

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post