Wandanda suke da sha'awa zasu iya shiga yanar gizon dake kasa, yanar gizon zai kasance sati biyu a bude yana da kyau masu bukata suyi kokarin cikawa da zarar yanar gizon ya fara aiki.
Mutane dubu biyar 5,000 ne gwamnatin tarayya ta bayar da umarni a dauka domin shiga aikin hukumar tsaron farin kaya ta najeriya NSCDC.
Apply now 👇
Hukumar tsaron farin kaya ta najeriya,ta bude yanar gizon daukar sabbabin ma'aikata wanda suke da sha'awa zasu iya shiga yanar gizon dake kasa yanar gizon sati biyu zata kasance a bude yana da kyau masu bukata su nema ku zasu dace mutane dubu biyar 5,000 ne gwamnatin tarayya ta bayar da umarni a dauka domin shiga aikin hukumar tsaron farin kaya ta najeriya NSCDC.
Ku tabbatar kun cike dukkan ka'idojin da hukumar ta gindaya domin samun nasarar shiga aikin.
Dalilai barkatai da suke hana mutanan mu samun duk wani abu da gwamnatin tarayya ta bude, rashin karanta sharudan dake cikin manhajar.
Wurin neman aikin ko cike wani abu daban da gwamnatin tarayya ta bude ba'a bukatar mutum yayi gagawa abu a hankali wurin cikewa, ka tabbata abun da suka tambaya kasa a wurin kada ka sanya musu abun da basu bukata ba.
Karanta ka'idojin yana da mutukar mahimmanci ga mai nema domin ta nan ne kadai zaka iya gano abubuwan daya dace ya nema dasu,dole mu bi a hankali mu natsu wurin karanta bayanai da hausa ko da turanci duk abun daka gani ba kayi tambaya ga wanda suka iya karatun turanci yafi dacewa ma kaje cafe idan har ka tabbata sun iya aiki zaka iya zuwa wurin su.
Shawara ga masu nema aikin ko wani abu daban. 👇
Ku sane wani bawa bai isa ya baku abun da Allah bai kaddara ba, kada kace ka dade kana nema baka samu ba ka cigaba da nema ka sanyawa zuciyarka cewa Allah ne kadai zai kaddara ka samu ko rashin samun.
komai lokaci ne a wannan rayuwar da kuke gani idan lokacin samun aikin ka baiyi ba wallahi tallahi ko shugaban kasa ne ya haifi ka ba zaka samu ba, idan ko lokacin samun aikin ka yayi zaka raina kaddarar silar samun aikin ka.
Komai zamuyi mu nemi shawarar iyaye don su sanya mu acikin addo'in su Allah ka cigaba da ciyar damu alheri.
Ga masu sha'awa sai su yi rijista ta wannan hanyar yanar gizo
Apply now
©Ahmed El-rufai Idris
Tags:
DAUKAR AIKI
