Sabuwar jaruma ce a Kannywood wadda ta sha alwashin samun nasara a burin da ta ke so ta cimmawa a game da shigowar ta wannan masana’anta nan ba da jimawa ba. A cewar ta, a yanzu har ta fara ganin hasken cikar burin nata.
A tattaunawar ta da Inuwar Labarai, jarumar ta bayyana cewa ita haifaffiyar Zariya ce, inda a nan ta yi makarantar firamare, sai kuma ta yi sakandare a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. Daga nan ta dawo Kano domin ta shiga harkar fim.
Amina, wadda ‘yar shekara 23 ce, ta ce, “A lokacin da zan shiga fim sai na zo Kano. Da man akwai gidan ‘yan’uwa na a Kano, don haka sai na dawo gidan da zama. Da haka na samu na shiga harkar fim ɗin.”
Ta ƙara da cewa, “A shekarar 2018 na shiga harkar fim, kuma daga lokacin zuwa yanzu na yi finafinai da dama. Amma dai waɗanda zan iya tuna sunan su akwai ‘Gidan Danja’, ‘Gidan Mato’ ‘Wata Makauniya’, da sauran su.”
Da wakilin mu ya tambaye ta yadda ta samu kan ta a matsayin jarumar fim, sai ta amsa da cewa: “To, gaskiya na ji abin wani iri na daban, saboda ka san a lokacin da ban fara fim ba, ai rayuwar da na ke babu wanda ya san da ni, to amma kuma da aka fara gani na a fim sai rayuwa ta ta sauya. Don haka ni ina ganin harkar fim ta sauya mani rayuwa, don a baya duk abin da na so na kan iya yin sa cikin sauƙi ba tare da wani ya sani ba, amma a yanzu duk abin da zan yi, to sai na duba na ga me zai jawo a gare ni a wajen mutane, tunda a yanzu duniya ta fara ganin abin da na ke yi. Wannan ya sa harkar fim ta sauya mani rayuwa ta.”
Akwai wani ɓangaren ma inda harkar fim ta sauya wa Amina rayuwa inda tace “A gaskiya, ni da man ina harkar kasuwanci. To sai ya zama ba a san ni ba, don haka ko da na saro kayan ma sai na daɗe ban sayar ba. Amma a yanzu da na fara harkar fim, sai na ƙara samun ciniki. Kuma ni da man babban buri na shi ne na yi amfani da fim na yi suna don ya zama na yi amfani da damar a wajen kasuwancin da na ke yi.
“To a yanzu ka ga daga na saro kaya ya ke ƙarewa, saboda wasu sun san ni a fim, su na sayen kayan saboda sun san ni ‘yar fim ce, ina burge su, don haka ina ganin burin da na ke da shi na shigowa harkar fim na same shi.”
Amina ta yi kira ga masu harkar fim da su gane akwai hanyoyi da dama da za su yi amfani da harkar fim domin su tsaya da ƙafar su ba tare da sun yi fim ba. “Kawai dai su yi amfani da damar da su ke da ita ta sunan da su ka samu a harkar fim, domin su gina rayuwar ta gaba ko da bayan sun bar harkar fim ɗin sun yi aure,” inji Amina S shehu
