Daga Comrade Yusha'u Garba Shanga.
"Dalilin da yasa har yanzu Ban koma ayi yaƙin neman zaben APC dani ba"
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana dalilin da ya sa har yanzu bai shiga yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC ba.
Kamar yadda rahoton DailyPost ya ruwaito, Gwamna Bello, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, ya halarci zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da Bola Tinubu ya lashe kwanakin baya.
Tun bayan ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu, gwamnan bai samu fitowa ba duk da naɗin da aka yi masa a matsayin kodinetan matasa na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.
Amma Bello ya ce ya daɗe yana yi wa Tinubu wasu ayyukan ƙarƙashin ƙasa, wanda hakan bai ba shi damar shiga cikin jirgin yaƙin neman zaɓen ba.
Ya zanta da Seyi Tinubu a ziyarar da ya kai ofishin sa da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi a ranar Alhamis.
Seyi ya jagoranci hukumar wayar da kan matasa ta ƙasa ta PCC zuwa gidan Lord Lugard da ke Lokoja, domin shirya tallafi ga mahaifinsa.
A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada cewa mutane na iya tunanin cewa ya daɗe a yanzu, yana mai cewa, amma da gaske yake yi wa Ɗan takarar APC aiki a ƙarƙashin ƙasa.
“Ina tare da Asiwaju (Tinubu). Ina yin wasu ayyuka na ƙarƙashin ƙasa domin samun nasarar Asiwaju a matsayina na Shugaba a jam’iyyar APC, shi ya sa ban bi jirgin yaƙin neman zaɓen sama da ƙasa ba. Wataƙila ba zan bi Asiwaju sama da ƙasa ba, amma abin da nake yi ya fi abin da ido ke gani.
"Zuwar 2023, za mu yi rikodin nasarar mu, zamu bayarda ƙarfin gwiwa, inji gwamna Bello ya bayyana wa Seyi Tinubu a matsayin “ƙaninsa” inda ya ce “Ni ne farkon Ɗan Asiwaju.”
Tun da farko, Seyi wanda shi ma ya je jihar Kogi domin rabawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a baya-bayan nan, ya ce Kogi na daga cikin Jihohin da ƙungiyar ta ware domin ziyarta da kuma tallafawa.
Ya kuma yabawa Bello da karɓon su, yayin da ya kuma godewa mataimakin gwamnan jihar, Edward Onoja da ya haɗasu da su Legas domin nuna goyon bayansa a yayin tafiya.
