Hukumar Kwallon kafa ta duniya ta baiwa kasar Morocco damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya na zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyoyin kasashen duniya da za’ayi a watan Fabarairu mai zuwa, saboda gamsuwa da rawar da kasar ta taka a Qatar da kuma tsare tsaren ta.
Wannan na cikin wata sanarwa da ta fito daga Shugaban Hukumar FIFA ta duniya Gianni Infantino, inda ya bayyana cewar sabon tsarin gasar da zai kunshi kungiyoyi 32 zai fara aiki daga shekarar 2025.
Infantino ya Kuma ce shekarun baya sun amince da shirin fadada yawan kungiyoyin da za su shiga gasar ta duniya wanda zai kunshi kungiyoyi 8 daga Turai, amma sai Annobar Korona ta hana gudanar da gasar bara a kasar China.
Shugaban hukumar yace sabon tsarin mai kungiyoyi 32 kamar gasar cin kofin duniya na kasashe zai fara a shekarar 2025.
A shekarar 2014, Morocco ta dauki nauyin irin wannan gasar wanda kungiyar Real Madrid ta lashe.
Yanzu haka dai zakarun nahiyoyin duniya sun hada da Flamengo ta Brazil da Al Hilal ta Saudi Arabiya da Wydad Casablanca na Morocco da Seattle Sounders ta Amurka da kuma Auckland City ta kasar New Zealand
Tags:
DANDALIN WASANNI


