Arsenal ta lallasa Totenham gida da waje a kakar bana

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta ci gaba da sa kaimi domin ta lashe Premier League na bana, bayan da ta doke Tottenham da ci 2-0 a yammacin jiya Lahadi.

Minti 14 da fara wasa Arsenal ta ci kwallo, bayan da Hugo Lloris ya ci gida, kuma karon farko da ya ci gida a wasa 354 da ya tsare raga a Premier League.

Sai kuma Mintuna na 36 kyaftin din Arsenal Martin Odegaard ya kara ta biyu, wanda ya zura kwallon ta takwas a bana kuma kwallon ta 18 kenan jimulla da yake da hannu aka zura a raga.

Da wannan samun nasara da Arsenal ta yi ta bai wa Manchester City tazarar maki takwas a teburin Premier League.

A wasan farko da ya gabata a cikin watan Oktoba, Arsenal ta ci Tottenham 3-1 a gasar Premier League a Emirates.

Rabon da Arsenal ta ci Tottenham gida da waje a Premier League tun a kakar 2013/14, inda Gunners ta ci 1-0 a Satumbar 2013.

A wasa na biyu kuwa a gidan Tottenham, Arsenal ta yi nasara da ci 1-0 a watan Maris din 2014.

Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier League da maki 47, sai City ta biyu mai maki 39, sannan Newcastle da Manchester United masu 38 kowacce.

Ranar Lahadi 22 ga watan Janairu, Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester United a Emirates a wasan Premier League.

Post a Comment

Previous Post Next Post