Ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party a mazaɓar Pengana a majalisar dokokin jihar Filato, Mathew Akawu ya rasu.
An bayyana cewa Akawu ya rasu ne a wani asibiti da safiyar yau Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa 'yan Jarida da faruwar lamarin a ranar Juma’a, ta ce tsohon shugaban makarantar ya rasu ne sa’o’i kadan bayan ya dawo daga bikin gargajiya a ƙaramar hukumarsa ta Bassa dake jihar filato.
Ɗan gidan ya ce, “Tabbas haƙiƙa gaskiya ne mun rasa ɗan takarar PDP a safiyar yau Juma’a.
“Bayan yaje bikinsu na gargajiya a Bassa ya dawo, sai jim kaɗan da hakan ya kamu da rashin lafiya, tare da dafe ƙirci namai ciwo.
"Daga nan aka garzaya da shi asibiti kuma a safiyar yau Juma'a ya mutu."
Abokin siyasarsa kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Jos ta Kudu a majalisar dokokin jihar, Fom Gwottson, ya bayyana rasuwar ɗan takarar PDP a matsayin abin ban tsoro.
Gwottson ya ce, “Daga cuɗanya daban-daban da muka yi tare, shi mutum ne mai tausayi kuma mai son mutanensa. Abin takaici ne cewa mun rasa shi a wannan lokacin. Lallai za mu yi kewarsa, kuma Allah Ya ji ƙansa.”
Mutuwar dan takarar PDP ya kawo adadin ‘yan takara biyu da suka mutu a jihar gabanin babban zaɓen mai zuwa a shekarar dubu biyu da goma sha ukku 2023.
RAHOTO DAGA:- Comrade Yusha'u Garba Shanga.
