Hanyoyi 2 Da Mace Zata Iya Yin Ciki Ba Tare Da Namiji Ya Kusanceta Ba

Ma'aurata

Daga Tsangayar Malam Tonga

A dabi'ance babu wata hanyar da aka san mace na iya samun ciki sai ta hanyar saduwa da namiji. Amma yanzu duniya ta sauya, masu illimi na kimiya tuni har sun samo wasu hanyoyin da mace take iya yin ciki ba tare da namiji ya kusance ta.

Wannan tsarin an samoshi ne saboda matan da suke da matsalar iya rike da a cikinsu har ya kosa. Haka kuma akwai matan da suke son haihuwa ba tare da sunyi aure ba ko suyi tarayya da namiji wajen mallakar abunda ta haifa ba. Wadannan dalilan sune suka taimaka wajen samar da wannan fasahar.
#Tsangayarmalamtonga

1:In-Vitro Fertilization: shi wannan tsarin ana amfani dashi ne ga matan da basa iya rike maniyi har ya samu cikar da zai zama da. Don haka sai a musu aikin da za a ajiye kwan a na'ura har sai ya kai munzalin da zata iya rike shi sai a cusa mata kwan daga nan sai ta ci gaba da rainon abunda ke cikin ta har ta haihu.

A irin wannan yanayin mata na zuwa idan ake sayar da irin wannan kwan domin dasawa a cikinsu idan basu da maza. Su kuma masu auren idan suna da wannan matsalar sai a ajiye maniyin mijin nata har sai ya kosa daga nan sai a dawo mata da shi cikin ta.

2:Insemination: shi wannan tsarin na ma'auratan da maniyin na miji bai iya samar da haihuwa. Ko kuma matan dake son haihuwa ba aure.

Ana daukan maniyin namiji ne a adana shi har sai yayi kosawar da zai iya zama a mahaifar mace sannan a cusa mata shi.
Idan kuma wacce batada aure ne sai ta je ta zabi kalar mutumin da take son maniyin sa a maajiyar adana maniyin da ake kira sparm bank. Ko kuma ta samu wani namijin ya bada maniyin sa. Daga nan sai a adana shi idan ya kosa a saka mata ta haifi abunta ba uba. Wannan shine tsarin da single mother ko mata masu auren junansu suke yi su haihu ba tare da miji ba.
Sai dai wadannan tsarin da muka ambata basu samu karbuwa a musulunce ba musamman ma na biyun.

Post a Comment

Previous Post Next Post