Kugiyar Mabiya Ahlulbaiti ta Siyasa sun ziyarci Sanata Barau a Kano

Gamayyar Kungiyoyin mabiya da masoya Ahlul bait mai suna AHLULBAYT NIJERIYA da ke yankin kananun hukumomin Kano ta arewa sun kai ziyarar girmamawa ga sanata Barau Ibrahim Jibril maliya, ziyarar sada zumunci da bayyana manufofin Kungiyar da mara baya ganin karatowar kakar zaben shekara ta 2023, da ta gudana a dakin taro na Paradise Hotel dake farm centre Kano a ranar Talata da ta gabata,
Taron wanda ya samu halartar wasu wakilai na kananan hukumomin mazabar sanatan na yankin Kano ta Arewa kamar karamar hukumar Tsanyawa, Kunchi, Gwarzo, Bichi Dawakin Tofa, Bagwai, Shanono, Rimin Gado, Tofa, Danbatta da kuma karamar hukumar Kabo da wasu daga cikin shugabannin Gamayyar ta jihar Kano, da kuma wakilcin Kungiyar ta kasa. 

Alh. Abba Danbatta wanda shi ne ma'ajin Gamayyar na jihar Kano sannan mai kula da yankin Sanatan Kano ta Arewa ya yabawa Santan akan irin aikace-aikacen al'umma da ya ke wa yankin.

A na sa jawabin, Hon. Adamu kabiru (Auduwa) ya yi godiya ga sanata akan baiwa wannan gamayyar damar kai masa ziyarar sannan yace " Ita wannan kungiya gamayya ce ta mabiya ahlul bait wato ('yan Shi'a) da kuma masoyansu, ciki harda bangaren sharifai da wasu daga cikin mu'assasoshi na bangarorin kungiyoyin Shi'a dama duk Wanda ya aminta da su, wadda suka hadu wuri daya don haduwa wajen marawa dukkan Dan takarar da ya aminta da fahimtar mu kuma ya yarda zai kare mana hakkokinmu da bamu damar dabbaka fahimtarmu ba tare da wata tsangwama ba idan yayi nasara a zabensa".
Ya kara da cewa "kuma cikin manufofinmu shi ne mu bamu da wata jam'iyya tsayayyiya a tafiyar wannan gamayya duk da a daidaikun mu muna da jam'iyyun da muke damawa da su to amma a gamayyance ba haka bane zamu Mara baya ne wajen samun nasarar Wanda zai kula da abubuwan da na fada a baya ciki kuwa harda kula da karatukan yaranmu, 'yancin mu da hakkokin mu a hukumance tare da daukar cewa muma 'yan kasa ne kamar kowa dole a kula da ilmin 'ya'yanmu kamar yadda kowa yake a kasa irin yadda tsarin mulki ya tanada, kuma banda wannan mu bamu da wata bukata data fita don mu ba siyasar jagaliyanci ce ko neman wani abu wajen dan takara ba". A cewar Hon.Auduwa

A nasa jawabin mai girma Sanata Barau jibril Maliya ya fara ne da godiya ga Allah da kuma godewa mahalarta wannan ziyarar sannan yace:

"Naji dadin wannan Ziyarar girmamawa da wannan gamayya ta kawo masa don gashi ma yaga fuskokin wadanda na sani da yawa, a shekarun baya da suka yi aiki tare kuma har aka samu nasara bai kara ganinsu ba, kuma basu taba zuwa neman wani abu wajensa ba, sai a yanzu na ya kara ganinsu Wanda hakan ya nuna cewa ana yi ne don cigaban al'umma ba wai don neman duniya ba, don ko wane gefe na waiga ina ganin fuskokin wasu daga cikinsu".

Ya cigaba da cewa "A kananan hukumomin da muke wakilta mun gina kananun tashar wutar lantarki guda uku, Samar da azuzuwan koyar da dalibai akalla guda dubu daya da Dari biyar (1,500), Samar da Jami'in gwamnatin tarayya (federal university), mun daga darajar makarantar kwalejin gwamnatin tarayya ta bichi (FCE Technical Bichi) da Kuma aikace aikace a harkar noma" Inji Sanata Maliya

Taron dai ya samu halartar manyan yan siyasa kamar su: Tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Fagge, kuma mai baiwa shugabanan kararmar Fagge shawara akan tattara haraji, Barrister Salisu Ahmad Fagge (Asi
Da mataimakawa shugaban Gamayya a Kano ta arewa Hon. Sabi'u Ibrahim Danbatta, da shugabar Mata Hajiya Zaharau Rabo, da sauran shugabanni da membobin wannan Gamayya maza da mata.

Post a Comment

Previous Post Next Post