Ni a yanzu ba na takarar Siyasa Fim din Izzar So kawai na sanya a gaba--Umar Hashim

Daga Ibrahim Hamisu

Fitaccen Jarumi a Masana'atar Kannywood Lawal Ahmad da aka fi sani da Umar Hashim a Fim din Izzar So, ya bayyana cewa shi yanzu ba takarar siyasa ba ce a gabansa, aikin fim din Izzar so da ayyukan mutane a ya sa gaba,


"Na fito takarar a baya Amma yanzu ba na takara saboda hankalina ya karkata akan wannan Fim din na Izzar So da ayyukan mutane, Amma dai har yanzu muna tare da yan Siyasa, kuma muna harkar siyasa tare da su"

A cikin shekaru biyu da fara yin Izzar so babu abinda za mu ce sai godiya, ya kara da cewa ya zuwa yanzu fim an fitar da na Dari Da Goma Sha Daya 111, 
Ya kuma jinjina da godewa makallata Fim din Izzar So, inda ya ce nasarar da aka samu a fim din ta fi ƙalubalen da aka fuskanta a Fim din,

"Babban jindadin dai shi ne yadda Fim Izzar so ke fadakarwa da ilmantarwa ta addini" Inji Lawan Ahamd

Post a Comment

Previous Post Next Post