Zan bayar da Ilimi kyauta da daƙile cin hanci da rashawa a jihar Kano – Abba Gida-gida

  

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP Abba Kabkir Yusuf ya ce babban abin da gwamnatinsa za ta sanya a gaba shi ne bayar da ilimi kyauta ga ‘yan asalin jihar.

Abba kabir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron muhawar ‘yan takarar gwamna da BBC ta shirya a jihar ranar Asabar.

A lokacin da mai gabatar da muhawar ya tambaye shi cewa ta ina zai samo kuɗin da zai bayar da ilimi kyauta a jihar a daidai lokacin da jihohi da dama ke kokawa kan matsin tattalin arziki?

Sai Abba Kabir ya ce ”Idan ka dakile cin hanci da rashawa a Kano to ka yi maganin matsalar”.

Ya kuma ce zai bunƙasa hanyoyin samun kuɗin shiga ta hanyar nemo taimako a wajen ƙungiyoyin bayar da tallafi domin tallafa wa ilimi a jihar.

Sannan Abba Kabir ya ce zai mayar da hankali wajen ɗaukar isassun malaman makaranta domin wadata jihar da malaman da take buƙata.

Post a Comment

Previous Post Next Post