Hankalin jama’a ya tashi bayan sace wasu manoma biyu Samuel Oladotun da Fashola Tobiloba a jihar Osun da kuma neman Naira miliyan 10 da masu garkuwa da su suka yi, rahotanni sun ce masu garkuwan sun karbi Naira miliyan 6 amma suka ki sakin wadanda suka yi garkuwa da su.
A cewar Vanguard, masu garkuwa da mutanen sun tsare tawagar mutane uku da suka kai kudin fansa a kan iyakar Kwara da Kogi a Epe inda suka bukaci karin kudi naira miliyan 24 kafin su sako mutanen.
An dai sace Samuel da Fashola ne a lokacin da suke dawowa daga gona a yankin Oke-Osun da ke Ileogbo, hedikwatar karamar hukumar Ayedire ta jihar Osun ranar Laraba.
Sai dai wata majiya daga iyalan ta shaidawa Vanguard cewa iyalan sun tattauna da masu garkuwa da mutane akan kudi naira miliyan 6 inda suka bukaci a kawo kudin fansa zuwa garin Epe dake kan iyaka da Kwara da Kogi.
"Duk da haka, daga baya sun yi amfani da lambar wayar mai sasantawa don isa ga iyalan kuma sun sanar da mu cewa an yi garkuwa da tawagar mutane uku, inda suka bukaci a kara Naira miliyan 24 don sako mutanen biyar," in ji majiyar.
Kakakin Royal Ambassador, kungiyar wadanda abin ya shafa na cocin Baptist ne, Olanihu Zakariah yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, “Abin bakin ciki ne da muka sanar da ku cewa wadanda suka karbi kudin fansa ga masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da ‘yan uwanmu Ambasada Samuel Oladotun. Haka kuma an tsare Fashola Tobiloba bayan ya biya kudin fansa ba tare da an sako ‘yan uwan biyu ba. Yanzu muna da mutum biyar (5) a cikin kogon masu garkuwa da mutane. Yanzu haka dai masu garkuwa da mutanen na neman a kara musu miliyan 24 domin a sako su.
“Muna matukar bakin ciki da faruwar lamarin. Ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga kowane memba da ya yi kira ga Allah a yanzu cikin ceto”.
RAHOTO:- Comrade Yusha'u Garba Shanga
