Ƙungiyar ƴan jaridu, NUJ ta ƙasa ta kori NOA daga Kungiyar


  Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya, NUJ , ta kori hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA daga kundin tsarin mulkin kungiyar

Rahotanni sun nuna cewa Taron wakilai na musamman da aka gudanar a Afficient event centre a Kano, wanda shugaban kungiyar na kasa Chris Isiguzo ya jagoranta, ya dauki wannan matakin, yayin taron duba da kundin tsarin mulkin kungiyar nuj.

kazalika wakilan da ke zaman sun ba da sanarwar cewa ba za a sake ba ma’aikatan NOA damar zama mamba na NUJ ba.

Za a ba wa wasu zaɓaɓɓun jami’an NOA damar cika wa’adin aikinsu.

Taron na watan Agusta ya kuma zartas da sabuwar dokar da ta haramtawa ma’aikatan yada labarai da aka yanke wa hukunci kasancewar ba ‘yan jarida ba ne daga yanzu an hana su shiga kungiyar ta NUJ.

Wakilan da suka halarci zaman sun kuma amince cewa kada a sake baiwa jami’an hulda da jama’a na kananan hukumomi matsayin mambobin kungiyar NUJ.

Post a Comment

Previous Post Next Post