A yammacin jiya Asabar ne gobara ta tashi a hedkwatar yan sanda ta Kano da ke unguwar Bompai.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost ta kuma bazu zuwa sashen kudi, dakin taro, ofishin Kakakin hedikwatar,PPRO da kuma ofishin mataimakin kwamishinan yan sanda (Admin) da sauransu.
Mai magana da yawon yan sanda na Jihar Kano Abdullahi Haruna ya shaidawa Freedom Radio cewa baa samu asarar rai ba, kuma ba ta taba wasu muhimman takardu ba,
Binciken da Manhaja ta tattara ya nuna cewa wutar ta shafi dukkan ofisoshin da ke saman benen hawa na daya, in banda ofishin kwamishinan.
“Mun yi kokarin kashe gobarar da ga ofishin Provost amma sai wutar ta bazu zuwa wasu ofisoshin. ‘Yan kwana-kwana sun isa wurin ne kusan sa’o’i 2 bayan tashin gobarar,” inji wata majiyarmu


