Wani Sabon Bala'in, 'Yan Bindiga Sun Kashe wata tsohuwa 'Yar Shekara 120 Da Wasu Mutane 5 A Sokoto
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a ƙauyen Raka da ke ƙaramar hukumar mulkin Tangaza a jihar Sakkwato inda suka ƙona gidaje da kayan abinci da dama kafin su tafi tare da wasu dabbobin gida da ba a bayyana adadinsu ba.
An tattaro cewa ‘yan fashin sun kashe wata mata ‘yar shekara 120 da wasu ‘yan unguwar a ƙallan mutane biyar.
Kamar yadda rahoton Daily Post ya ruwaito, da aka tuntuɓi hakimin yankin, Alhaji Sa’idu Wakili ta wayar tarho, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce duk da cewa ba a yi garkuwa da kowa ba, amma ‘yan fashin sun ƙona kashi biyu bisa uku na gidaje da kayayyakin abinci, sannan kuma sun yi awon gaba da shanaye.
Ya Buƙaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su ƙara zage damtse wajen magance matsalolin tsaro a yankin dama ƙasar baki ɗaya.
Hakimin ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su samar da gagarumin hanyoyin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Tangaza, Alhaji Ibrahim Lawal Junju, tare da mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tituna, Engr. Mai Damma Tangaza ya ziyarci al’ummar garin tare da jajanta wa mutanen ƙauyen sannan kuma ya yi alƙawarin mika sakamakon bincikensa ga gwamnati domin taimakon waɗanda abin ya shafa.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma hukumomin tsaro har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
RAHOTO:- COMRADE YUSHA'U GARBA SHANGA.
